Zaben raba gardama a Mauritaniya | Siyasa | DW | 21.07.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben raba gardama a Mauritaniya

A wannan Juma'ar ce aka soma neman kuri'u a shirin zaben rabagardama kan kundin tsarin mulki a kasar Mauritaniya. Zaben zai gudana a ranar biyar ga watan gobe. Sai dai wani bangaren adawar kasar ya zabi kauracewa.

A cikin wani babban zauran taro da ke tsakiyar birnin Nouakchott, ministan harkokin wajen kasar ta Mautaniya Isselkou Ould Ahmed Izidbih, ya dukufa wajen fadakar da jama'a dalilan kawo sauye-sauye ga kundin tsarin mulkin kasar, musamman batun soke majalisar dattawa, daya daga cikin majalisun dokoki biyu na kasar. Zaben rabagardaman na kasar Mauritaniya ya kuma shafi batun sake tutar kasar, inda a ranar biyar ga watan na Agusta za a gabatar wa 'yan kasar sabuwar tutar mai dauke da wasu layuka biyu masu launi ja bayan launi da aka saba gani bisa tutar kasar ta kalar rawaya ko kuma tsanwa. Sai dai a cewar bangaran gwamnati, wannan sabon launi na ja da ake son karawa a turar kasar ta Mauritaniya, na nufin tunawa da 'yan mazan jiya da suka rasu lokacin yaki da turawan mulkin mallaka.

Wannan mataki na zaben raba gardama, ya biyo bayan yin watsi da majalisar dattawan kasar ta yi na batun sauye-sauyen kundin tsarin mulki, wanda hakan ya sanya gwamnatin gabatar da batun ga 'yan kasa baki daya. Sai dai masu adawa sun ce sam bai cancanta ba. 

Daga bangaran masu na'am da gyaran kundin tsarin mulkin, ana ganin maimakon  'yan adawa su shiga yakin neman zabe domin neman magoya bayansu su zabi kin amincewa da tsarin, sun zabi kawai su kauracewa zaben don boye rashin magoya bayan da suke fama da shi. Sai dai sauye-sauyen da ake son kawo wa a kundin tsarin mulkin kasar ta Mauritaniya bai shafi batun wa'adin mulkin shugaban kasa ba, da ya kayyade wadin mulki biyu. Firaministan kasar ta Mauritaniya ya ce batun wa'adin mulkin shugaban kasa shi ma ya danganta da abin da al'ummar kasa take so. Al'ummar da ya ce akasarinta na goyon bayan sake tsayawar takarar shugaba Mohamed Ould Abdel Aziz a zabe mai zuwa na shekarar 2019.