1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Jaridun Jamus sun mayar da hankali kan zaben Najeriya

Mohammad Nasiru Awal SB
March 1, 2019

A labarai da sharhin da suka yi jaridun Jamus gaba daya sun mayar da hankali ne kan babban zaben da aka gudanar a Najeriya da Shugaba Muhammadu Buhari ya samu nasara a karo na biyu.

https://p.dw.com/p/3EJBz
Nigeria, Abuja: Präsident Muhammadu Buhari begrüßt seine Unterstützer
Hoto: Reuters/B. Omoboriowo

 

A sharhin da ta rubuta mai taken "Nauyi a kan tsofaffin Maza" jaridar Süddeutsche Zeitung ta ce a shekarar 2015 lokacin da Muhammadu Buhari ya lashe zabe an yi doki da kyakkyawan fata musamman alkawarin da ya yi na kawo sauyi da yaki da cin hanci tare da ganin an yi adalci kan arzikin man fetur din kasar. Amma haka ba ta cimma ruwa ba. Duk da haka dai 'yan Najeriya sun sake zaben Buhari a sabon wa'adin shekaru hudu na mulki, sai dai shugaba ne da shekarunsa suka haura a kasar da mafi yawan al'umarta matasa ne, wadanda suka fidda tsamanin samun wani abin kirki daga shugabannin siyasa. Fata shi ne nan da wani lokaci mai zuwa tsoffin jinin za su ja baya su ba wa sabbin jini wuri.

Nigeria - Wahl verschoben
Hoto: picture alliance/AP Photo/S. Alamba

Manya-manyan matsaloli inji jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tana mai cewa ba sabon abu ne zargin tabka magudi a zaben Najeriya domin da wuya a samu zabe na gaskiya da adalci a nahiyar Afirka. Sau da yawa kuma masu sa ido a zabe murna suke idan ba a samu salwantar rayuka masu yawa ba.

Sai dai duk da asarar rayuka da aka yi a zaben na Najeriya shugaban tawagar kungiyar tarayyar Afirka da suka sa ido a zaben na Najeriya, Hailemariam Desalegn da ke zama tsohon Firaministan kasar Habasha ya ce zaben ya gudana cikin kwanciyar hankali da lumana. Amma jaridar ta nuna shakku ko Shugaba Buhari da ke nuna alamar gajiya saboda yawan shekaru zai iya magance manya-manyan matsalolin da kasar da ta fi yawan al'umma a Afirka, ke fuskanta wato kamar na tsaro da rashin aikin yi tsakanin matasa da cin hanci da rashawa.

Nigeria Präsidentschaftswahlen
Hoto: picture-alliance/AP Photo/S. Alamba

Ita ma jaridar Neue Zürcher Zeitung ta yi tsokaci a kan siyasar ta Najeriya tana mai cewa Buhari ya sake lashe zaben shugaban kasa abin da ke nufin kasar za ta samu tabbaci na kwanciyar hankali, amma babu mai murna saboda shugaban ba shi da cikakken karfi na aiwatar da sauye-sauye a Najeriya. Lokacin da ya ci zabe a 2015 an yi kyakkyawan fatan cewa shi ne kadai zai iya yakar Boko Haram da cin hanci, amma hakan ba ta samu ba. Jaridar ta ce yadda cin hanci ya yi katutu a kasar, ana bukatar juyin juya hali na hakika kafin a sauya tsarin. Shi ma babban abokin hamiyarsa wato Atiku Abubakar wanda ya yi alkawarin farfado da tattalin arziki da sayar da kamfanin man fetur na kasar sai dai ko shi din ma da babu tabbas ko zai iya aiwatar da sauye-sauyen ko da ya ci zaben.

A karshe sai jaridar Die Tageszeitung ta ce ba ta sauya zane ba a Najeriya, Buhari zai ci gaba da mulki. Ta ce godiya ta tabbata ga karancin yawan wadanda suka kada kuri'a musamman a manyan biranen kasar kamar Legas, an sake zabar shugaba mai ci, wato har yanzu tsoffin 'yan siyasar ne ke jan zarensu, abin da kuma ke bakanta wa matasa rai da ke ganin an mayar da su saniyar ware a harkokin siyasar Najeriya.