1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zaben maye gurbin Firaminista Boris Johnson

Binta Aliyu Zurmi
July 13, 2022

'Yan jam'iyyar Conservatives a Birtaniya sun gudanar da zagayen farko na zaben wandanda za su yi takarar kujerar Firaministan Birtaniya Boris Johnson.

https://p.dw.com/p/4E5aA
Conservative Party leadership
Hoto: Axel Heimken/dpa/picture alliance

A zaben da aka gudanar, mutane biyu basu kai ga yin nasara ba bisa gaza samun kuri'u 30 kamar yadda aka bukata.

Tsohon sakataren lafiya Jeremy Hunt tare da Nadhim Zahawi na daga cikin wadanda aka fidda a wannan zabe na fidda gwanin da za maye gurbin Firaminista Boris Johnson.

Rishi Sunak dai shi ne ya zo na farko da kuri'u 88 yayin da ministan cinikayya Penny Mordaunt ya zo na biyu da kuri'u 67 ita kuma sakatariyar harkokin wajen Birtaniya Liz Truzz ta sami matsayi na uku bayan samun kuri'u 50.

A gobe Alhamis za a ci gaba da zaben har sai an kai ga mutum biyu kacal inda za su fafata a tsakaninsu don zama Firaministan Birtaniya bayan Boris Johnson.