1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shirin zaben Mali a cikin yanayin dar-dar

Ramatu Garba Baba GAT
July 24, 2018

A Mali, lokacin da ya rage kasa da mako daya a gudanar da zaben shugaban kasa gwamnatin ta baza jami'an tsaro akalla dubu 11 a fadin kasar domin tabbatar da tsaron lafiyar jama'a.

https://p.dw.com/p/321eB
Mali Wahl in Mali 2018 | Wahlplakate
Hoto: DW/K. Gänsler

Masu sharhi na ganin kamar da wuya matakin ya baza jami'an tsaro ya yi tasiri ganin irin yadda kungiyoyin 'yan ta'adda suka samu gindin zama a Mali da ma yawaita kai hare-hare har a barikokin sojoji a baya bayan nan. Manyan 'yan takara da za su fafata a zaben su hada da shugaba mai ci Ibrahim Boubacar Keita da kuma babban abokin hamayarsa Soumaila Cisse. 


Al'ummar birnin Gao na arewacin kasar na cike da fargabar barkewar rikici kamar yadda ake ci gaba da samu a sassan kasar. Alkalumma na nuni da cewa tun daga farkon wannan shekarar mutane kusan dari uku ne suka rasa rayukansu a sanadiyar rikice-rikice a kai a kai a tsakanin al'umomi ko kuma daga mayakan kungiyoyin masu da'awar jihadi. Wannan ta sanya kwamitin kula da kare hakkin dan Adam na Majalisar Dinkin Duniya ya yi gargadi kan daukar matakin gaggawa don shawo kan rikicin da ma daukar mataki kan masu aikata wadannan laifuka 
 
Shekaru biyar ke nan da aka jibge rundunar sojin Faransa a kasar da zummar yakar mayakan Kungiyar  al-Ka'ida da ke a arewacin kasar. Ana dai ganin an samu ci gaba, amma daga baya sai ya kasance ci gaban mai hakar rijiya don kuwa a yanzu haka sha'anin tsaro ya tabarbare duk kuwa da kasancewar sojojin da kuma tallafin da kasar ke samu na kudi daga kasashen waje don gudanar da ayyukan tsaro musanman a yankin na Gao. 

Mali Wahl in Mali 2018 | Anhänger von Cheick Modibo Diarra in Sikasso
Hoto: DW/K. Gänsler


Yanzu haka dai wannan barazana ta tsaro da yankin na Gao ke fuskanta ta hana wasu mazaunansa fita samun katin zabe. A don haka Jama'a ke bayyana fatan ganin kafin zaben na ranar 29 ga wannan wata na Yuli, lamuran tsaro sun inganta ta yadda za su iya fita kada kuri'a ba tare da wani tarnaki ba.