Zaben Malawi: Kammala yakin neman zabe | Siyasa | DW | 20.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben Malawi: Kammala yakin neman zabe

Gabanin soma gudanar da zaben kasar Malawi, 'yan siyasa sun karkare yakin neman zabe da alkawura daban-daban don janyo hankulan masu zabe.

 Peter Mutharika und Saulos Chilima (Getty Images/A. Gumulira)

Peter Mutharika da Saulos Chilima yayin yakin neman zabe a shekara ta 2014

Batun da ya fi daukar hankulan 'yan Malawi da zarar an ambaci Mary Chilima uwargidan mataimakin shugaban kasa Saulos Chilima shi ne iya kwalliya da kuma saukin kanta, sai dai a wannan karon wakar gambara da ta saki don jan hankulan jama'a  a yayin yakin neman zaben da mijinta Saulos ke yi a kokarin zama shugaban kasa,  ya zo wa al'ummar kasar da mamaki. Ta yi amfani da wakar ta rap don jan hankulan matasan kasar wanda sune kaso 70 cikin100 na al'ummar Malawi. Wakar mai taken “Tikupatsani” ma'ana "za mu aiwatar," ta kunshi baituka da ke cike da alkawura na samarwa matasa aikin yi da damar kasuwanci da ilimi. Tuni bidiyon wakar ya karade shafukan Internet kamar kafofin sada zumunta na watsapp da Facebook da twitter.

Muhawara ta barke inda da dama ke yaba mata, wasu na ma ganin ta dace da uwargidan shugaban kasa, ga Raphael Nedi da ya saurari wakar, ya ce shakka babu wakar ta birge shi, sai dai ba ta kai ga sauya masa ra'ayi na ya zabi Saulos Chilima ba. Ita kuwa Benadetta ta jinjinawa Uwar-gida Chilima bisa wannan kokari, da ta ce ya dace ya zamo abin koyi ga sauran mata wajen kara azama su marawa mazajensu baya, amma ta wata hanya daban ba waka ba. To da ya ke gidajen radiyon kasar da dama ba su da 'yancin tallata wakoki na siyasa, duk da haka  suna fuskantar matsi daga 'yan kasa na lallai a saki wannan waka ta Mrs Saulos. 'Yan takara uku ne dai ke sahun gaba a fafatawar neman kujerar shugabancin kasar, jam'iyya mai mulki ta Democratic Progressive Party(DPP) ta Shugaba Peter Mutharika sai jam'iyyar adawa ta Congress Party (MCP) da ke da Lazarus Chakwera a matsayin dan takara da kuma United Transformation Movement (UTM) da Saulos Chilima ke takara. Wannan dai shi ne karo na biyar da Malawi ke gudanar da zaben tun bayan komawa kan turbar mulkin dimokradiyya.

Sauti da bidiyo akan labarin