Zaben majalisar Mali ya bar baya da kura | Siyasa | DW | 25.11.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben majalisar Mali ya bar baya da kura

Rahotannin sun nunar da cewa an fukanci tsaiko na katin zabe da satan akwatunan zabe a Arewacin Mali. Sai dai masu sa sun yaba yadda zaben 'yan majalisa ya gudana a kasar.

Rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta na ci-gaba da daukan matakan tsaro a arewacin Mali domin hana barkewan tashin hankali a lokacin da ake kidaya kuri'un da aka kada a ranar lahadi. Wannan mataki dai ba ya rasa nasaba da rikicin da Abzunawa da ke neman ballewa suka tayar a ranar zaben na 'yan majalisa, inda suka hana kada kuri'a a garin Talataye da ke gabashin birnin Gao. Hakazalika sun farfasa maduban wasu motoci tare da ji ma wata mace daya rauni a birnin Kidal da ke zama matattararsu.

An tafka kura-kurai a zaben Mali

Ministan shari'a na Mali ya ce gwamnati ba za ta kyale wadanda suka hadassa fitina ranar zabe ba tare da daukan matakan da suka wajaba a kansu ba. Hasali ma dai gwamnati ta fara nemansu domin ta kamasu tare da gurfanar da su gaban kuliya. Ko da ita ma Sandrine Blanchard, ma'aikaciyar sashen Faransanci na Deutsche Welle wacce ta shaidar da zaben na Mali, sai da ta ce an sace akwatuna a wasu sassa na kasar.

Malian security forces check voters before they enter to vote in the parliamentary election in Lafiabougou, Bamako November 24, 2013. REUTERS/Adama Diarra (MALI - Tags: ELECTIONS POLITICS)

Matakn tsaro ba su hana tashin hankali nan da can ba a Mali

"Fadace-fadace da ba su taka kara sun karya ba aka fuskanta a arewaci. Sannan kuma an sace akwatunan zabe a kananan hukumomin Goundam da kuma Lere. Wasu 'yan bindiga ne suka aikata wannan danyen aiki, lamarin da ke nuna cewa akwai jan aiki wajen tabbatar da tsaro ko da a lokacin zabe ne."

Mutane kalilan suka kada kuri'a

Ba a dai bayyana alkaluma game da yawan 'yan Mali da suka kada kuri'unsu domin zaben wadanda za su wakilcesu a majalisa ba. Amma kuma gamayyar kungiyoyi da suka sa ido a zaben wato POCE a takaice ta kiyasta cewa kashi 30% na al'umar kasar ne suka je runfunan zabe domin sauke nauyin da ke kansu. Lamarin da ya zama komabaya idan aka kwatanta da zabe shugaban kasa inda kashi 50 % na 'yan Mali suka yi tururuwa a gaban runfunan zabe.

Ita kuwa tawagar masu sa ido na kasashen Turai ta nuna gamsuwarta da yadda zaben 'yan majalisan Mali ya gudana, bayan da ta ziyarci kashi uku cikin biyar na runfunan zabe da ke cikin yankunan takwas na Mali. Sai dai a cewar Sandrine Blanchard babban kuskure da aka tafka a shirin zaben na Mali, shi ne mantawa da katin madugun 'yan adawan kasar Soumaila Cisse, wanda shi ne ya zo na biyu a zaben shugaban kasa.

"Daga cikin wadanda suka ci karo da matsalar kada kuri'a har da Soumaila Cisse, wanda ya kaura zuwa kusa da Toumbouctou lokacin da aka yi yakin neman zabe. Sai dai kuma a lokacin da ya je kada kuri'a, ya farga cewa ba a rubuta sunanshi ba. Rundunar kiyaye zaman lafiya ta MINUSMA ce ta je da jirgin sama zuwa Bamako inda ta dauko takardar masu kada kuri'a, domin baiwa Soumaila Cisse da iyalinshi damar zabe a Nyafounke kamar yadda ya kamata."

Jam'iyyar IBK na fatan zuwa ta daya

Mali's president Ibrahim Boubacar Keita casts his vote at a polling station in Bamako, on November 24, 2013. Malians voted on November 24 in parliamentary elections intended to cap the troubled west African nation's return to democracy but overshadowed by the threat of Islamist reprisals. AFP PHOTO / HABIBOU KOUYATE (Photo credit should read HABIBOU KOUYATE/AFP/Getty Images)

Jam'iyyar shugaba Keita na fatan samun rinjaye a zaben Mali

Hukomomin da aka dora wa alhakin shirya zaben na Mali sun nunar da cewa za a fara samun alkaluman farko a wannan litinin. Jam'iyyar RPM ta shugaban kasa Ibrahim Boubacar Keita na fatan samun rinjaye a majalisar ta dokoki. Yayin da jam'iyyar URD ta madugun 'yan adawa Soumaila Cisse ke fatan zama ta biyu a majalisar. 'Yan Mali miliyan shida da dubu 500 ne suka cancanci kada kuri'a a zaben da ke zama matakin karshe na mayar da Mali kan turbar demokaradiya.

Idan dai za a iya tunawa kasar ta Mali ta yi fama da rikici na siyasa bayan juyin mulki da sojoji suka yi a watan Maris na 2012. Wannan lamarin dai ya baiwa masu kaifin kishin addini da ke da alaka da kungiyar Al-Qa'ida damar mamaye arewacin kasar. Sai dai sojojin Faransa da kuma wasu na kasashen Afirka sun far musu a watan Janairun wannan shekarar inda suka fattakinsu, tare da sake bai wa Mali damar zama tsintsiya madaurinki daya.

Rahoto cikin sauti na kasa

Mawallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Umaru Aliyu

Sauti da bidiyo akan labarin