Zaben kananan hukumomi a Guinea | Labarai | DW | 04.02.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben kananan hukumomi a Guinea

'Yan kasar Guinea Conakry milyan biyar da dubu 900 ke kada kuri'a a zaben kananan hukumomi, inda tun da misalin karfe takwas na safe masu zabe suka yi dogon jeri a mazabu.

Äquatorialguinea 2016 Präsidentschaftswahl (Getty Images/AFP/STR)

Zabe a kasar Guinea

Da wajejen karfe shida na yamma ne dai ake sa ran rufe runfunan zaben, sai dai ga mutane da dama daga cikin 'yan kasar ta Guinea, wannan shi ne karo na farko da suke zaben na kananan hukumomi, ganin cewa zabe na baya an yi shi ne a shekara ta 2005 shekaru 13 da suka gabata a lokacin mulkin Janar Lansana Conté, wanda ya shugabanci kasar daga shekara ta 1984 zuwa 2008. Wanda a lokacin jam'iyyarsa ta lashe zaben da kashi 80 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada, abun da ya basu jagorancin kananan hukumomi na birane 31 daga cikin 38, sannan na karkara 241 daga cikin 303 da ake da su a kasar ta Guinea.

An dai sauya shugabannin kananan hukumomin bayan cikar wa'adin mulkinsu a shekara ta 2010 a karkashin mulki shugaba mai ci yanzu  Alpha Condé bayan da aka yi shekaru biyu na mulkin rikon kwarya na soja.