Zaben kakakin majalisar dokokin Jamus | Labarai | DW | 22.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben kakakin majalisar dokokin Jamus

An sabonta wa'adin mulkin kakakin majalisar Jamus Norbert Lammert a zaman farko da Buntestag ta yi tun bayan zaben 'yan majalisa a watan satumban da ya wuce.

Majalisar dokokin Jamus ta Bundestag ta fara zamanta na farko tun bayan zaben 'yan majalisa da aka gudanar kwanaki talatin da suka gabata a wannan tarayya . Tuni ma dai ta gudanar da zaben kakakinta inda Norbert Lammert mai barin gado ya samu damar yin tazarce. Dan siyasan mai shekaru 64 wanda ya fito daga jam'iyyar CDU ta Angela Merkel ya samu kuri'u 591 yayin da takwas daga ciin 'yan majalisa suka yi rowar kuri'unsu, sauran 26 kuma suka ki amincewa da shi.

Wannan dai shi ne karo na uku da Lammert ya zama shugaban majalisa, da ke zama mukamin na biyu mafi daraja a Jamus baya ga na shugaban kasa. A shekara ta 2005 shekaru takwas da suka gabata ne Lammert ya fara zama kakakin Bundestag.

Wallafi: Mouhamadou Awal Balarabe
Edita: Saleh Umar Saleh