Zaben Gini Conakry ya bar baya da kura | Labarai | DW | 04.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben Gini Conakry ya bar baya da kura

'Yan adawa a kasar Gini Conakry da ke yankin yammacin Afirka sun nace kai da fata sai a soke sakamakon zaben 'yan majalisa da aka gudanar idan ana so a zauna lafiya.

'Yan adawa a kasar Gini Conakry da ke yankin yammacin Afirka sun nemi soke sakamakon zaben da aka gudanar ranar 28 ga watan Satumba, wanda suka zargi an tafka kazamin magudi. Gamayyar jam'iyyun adawa ne suka fitar da sanarwar inda suka zargi mahukunta da arigizun kuri'u.

Wannan kira ya ci karo da karfin gwiwar jam'iyya mai mulki, wadda ta ce za ta samu gagarumar nasara, bayan ayyana cikekken sakamakon zaben. Kusan duk jam'iyyun adawa sun zargi jam'iyyar RPG ta Shugaba Alpha Conde da magudin zabe, yayin neman shiga majalisar dokokin kasar mai kujeru 114.

Tun da farko an nuna fatar zaben zai dinke rikicin siyasar da kasar ta Gini Conakry ta kwashe shekara da shekaru tana fama da shi.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe