Zaben EU: Zabi tsakanin masu sassauci da masu tsattsaurar ra′ayi | Siyasa | DW | 24.05.2019
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zaben EU: Zabi tsakanin masu sassauci da masu tsattsaurar ra'ayi

Zaben 'yan majalisun dokokin Tarayyar Turai da za a gudanar a karshen wannan wata na Mayu da muke ciki, zai bayyana sabuwar alkiblar da nahiyar ke kai. Komawa kan turbar tsantsan kishin kasa ko kuma karuwar sajewa.

Batun samar da ayyukan yi da matsalar 'yan gudun hijira da dumamar yanayi da kuma siyasar kasuwanci, na daga cikin batutuwa da nahiyar Turai ke takawa gagarumar rawa a kansu a duniya. Wadannan dai sune batutuwa da suka zamanto tilas kungiyar Tarayyar Turai EU ta mayar da hankali a kansu a shekaru masu zuwa, a cewar jam'iyyar Established Europe-friendly.

Gumurzu tsakanin 'yan takara a zaben da ke zaman kalubale ga nahiyar Turai

Manyan 'yan takara a zaben na wannan wata na Mayu dai sun hadar da Manfred Weber na jam'iyyar Christian Democrats da kuma Frans Timmermans na jam'iyyar Socialists ta masu ra'ayin gurguzu, 'yan takarar da ra'ayinsu ya kusan zama daya. Baki dayansu dai na son sake hada kai da Afirka da kuma mayar da hankali kan kara zuba jari a kasashen masu neman mafaka na asali. A ta bakin Weber na jam'iyyar Christian Democrats suna jin dadin yadda Turai take a yanzu. Ya ce. "Muna tunkarar zabe a wannan nahiyar a ranar 26 ga watan Mayu. Wannan Turai din da muke ciki yanzu, Turai ce mai kyau kuma ba za mu zuba ido mu bar masu matsanancin kishin kasa da muke fama da su, su wargazata ba."Sai dai ga 'yan jam'iyyar Right-wing populists ta masu matsanancin kishin kasa, tilas a takawa 'yan gudun hijira birki kamar yadda ministan harkokin kasashen ketare na Hangari Peter Szijjarty ke cewa: "A wajenmu masu adawa da 'yan gudun hijira da muke da rinjaye, batu ne da ke da matukar muhimmanci a garemu, kuma Hangari za ta taimaka."

Damuwa a kan masu tsatsauran ra'ayi da ka iya taka rawa a zaben


Firaministan Hangari da ke zaman dan jam'iyyar masu matsanacin kishin kasar,Viktor Orban dai na nuna damuwarsa kan siyasar masu tsattsauran ra'ayi da yake wakilta da kuma ta masu sassaucin ra'ayi, inda ya  yi zargin cewa wadanda ke da sassaucin ra'ayin na son su musuluntar da al'ummar Turai ta hanyar budewa 'yan gudun hijira kofofinsu.