Zaben Bene: Firmanista ya amince da shan kayi | Labarai | DW | 21.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaben Bene: Firmanista ya amince da shan kayi

Sakamakon farko da ya fira fita a ranar Lahadin dai ya nuna cewa Patrice Talon ya samu gagarumin rinjaye kamar yadda Zinsou ya fada wa kamfanin dillancin labaran Faransa.

Fitaccen dan kasuwannan na kasar jamhuriyar Benin Patrice Talon ya yi nasara a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa da aka yi a ranar Lahadi. Babban dan adawarsa firaminsta Lionel Zinsou ya bayyana haka a zantawa da kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP kafin bayyana sakamako daga hukumar zaben kasar.

Sakamakon farko da ya fara fita a ranar Lahadin dai ya nuna cewa Patrice Talon ya samu gaggarumin rinjaye kamar yadda Zinsou ya fada wa kamfanin dillancin labaran, wanda a cewarsa tuni ya kira Talon ta wayar tarho tun a daren na Lahadi dan yi masa murna inda zai maida hankali ga batun yadda za a kai ga mika mulki.

Kimanin mutanen kasar ta jamhuriyar Benin miliyan hudu da dubu dari bakwai ne dai suka cancanci kada kuri'a dan zaben wanda zai gaji shugaba Thomas Boni Yayi da ya kammala wa'adin mulkinsa ba tare da neman kwaskwarima ba a kundin tsarin mulkin kasar, kamar yadda wasu shugabannin na Afikra ke yi.