Zabe ya gudana cikin kwanciyar hankali a Mali | Siyasa | DW | 11.08.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Zabe ya gudana cikin kwanciyar hankali a Mali

Hukumar Zabe mai Zaman Kanta da Gamayyar kasa da kasa sun gamsu da yadda zaben shugaban kasa zagaye na biyu ya gudana duk da 'yan kura-kuren da aka samu.

Kombibild Keita und Cissé. Links: ARCHIV - Ex-Ministerpräsident von Mali Ibrahim Boubacar Keita spricht zu seinen Unterstützern in seinem Hauptquartier in Bamako, Mali am 04.05.2013. Am 11.08.2013 findet die Stichwahl zwischen Boubacar Keïta und Ex-Finanzminister Cissé statt. Foto: EPA/TANYA BINDRA +++(c) dpa - Bildfunk+++ Rechts: ARCHIV - Soumaila Cisse, Präsidentschaftskandidat in Mali, spricht am 02.05.2013 zu seinen Unterstützern in Bamako, Mali. Am 11.08.2013 findet die Stichwahl zwischen dem früheren Ministerpräsidenten Keïta und Cissé statt. Foto: EPA/TANYA BINDRA +++(c) dpa - Bildfunk+++

Präsidentschaftswahlen Mali

Al'umar Mali na ciki da wajen kasar, sun kada kuri'a wannan Lahadi, a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa, domin tantance wanda zai shugabancin kasar tsakani Ibrahim Boubacar Keita da Soumaila Cissé.

Rahotani daga sassa daban-daban na kasar Mali sun tabbatar da cewa zaben ya wakana lami lafiya.Duk da ruwan sama da aka tafka bai hana mutane ba su hito da himma domin raba gardama tsakanin 'yan takara biyu da ke zawarcin kujera shugaban kasar Mali.

Shugaban Hukumar zabe mai zaman kanta Mamadou Diamoutani ya baiyana shirin da suka tanada wanda ya kai su wannan nasara:

"Hukumar Zabe mai Zaman Kanta tare da ofishin ministan cikin gida, mun yi nazarin kurakuren da su ka wakana a zagayen farko, kuma mun dauki matakan magance su a zagaye na biyu.

Kowa ya shaidi haka.Misali a ko wace runfar zabe, akwai wakilin Hukumar Zabe, sannan kuma mun horar da wasu mutane, wanda mu ka bari cikin shirin ta kwana, ko da wani daga mutanen da mu wakilta ba zai sami damar zuwa ba"

An gudanar da zaben tare da sa idon 'yan kallo daga ciki da wajen kasar Mali.

Kadire Desire Ouedrago shine shugaban Hukumar zarsatwa ta kungyiar ECOWAS ya ce sun gamsu da zaben na Mali:

" Duk runfunan zaben da muka ziyarta mun isko suna cikin aiki ba tare da matsaba.An kai kayan aiki,da jami'an hukumar zabe da kuma wakilan 'yan takara.Mun gamsu da tsarinda akayi".

An cimma wannan sakamako tare da hadin kan jama'ar kasa wadda ta kosa da halin da Mali ta shiga kamar yadda wannan dan kasa ya baiyana:

Dalilin da ya sa na hito in zabe shine in ba da gudunmawata wajen ginin kasa.Kowa ya shaidi yadda kasarmu ta wahala.Yanzu da dama ta samu ta kubuto ta daga halin da ta tsinci kanta, yauni ya rataya ga duk dan kasa ya yi zabi shugaba na gari wanda zai iya hidda surfe daga ruwa".

Duk wani mai farin ciki da wannan zabe, baya ya ke ga shugaban rikwan kwayra Pr Diouncounda Traore, wanda ya baiyana godiya game da yadda gwamnatinsa ta fuskanci kalubalen shirya zaben

" Ai tuni za a iya cewar rikwan kwarya ya yi nasara.Yanzu za mu shiga wani saban babe na tarihin kasar Mali, wato gina kasa da kuma hadin kanyan kasa".

Saidai duk da ikirarin nasara da hukumomi ke yi zaben na jiya kamar zagayen farko ya ci karo da matsaloli hasali ma na katinan zabe.A halin yanzu dai jama'ar kasa na cikin jiran sakamako.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Abdourahmane Hassane

Sauti da bidiyo akan labarin