1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

300514 Wahlkampf Syrien

June 2, 2014

Duk da yakin da ya mamaye kasar ta Siriya da kuma miliyoyin 'yan kasar da ke gudun hijira, a wannan Talata ake gudanar da zaben shugaban kasar.

https://p.dw.com/p/1CAkH
Libanon Syrien Demonstration syrischer Flüchtlinge gegen Präsidentschaftswahl von Bashar al-Assad
Hoto: Reuters

Gdan telebijin kasar ta Siriya ya yi ta watsa shirye-shirye game da zaben inda yake nuno sojoji dauke da makaman yaki suna kira ga al'umma da su yi amfani da kuri'arsu a matsayin makami a zaben na wannan Talata. Sabon abu ga wannan zaben shi ne amincewa da takarar mutum fiye da guda. Sabuwar dokar zaben Siriya ta ce dole ya zamana dan takara na zaune cikin kasar shekaru 10 a jere sannan kotu ba ta taba samunsa da wani laifi ba, kana kuma yana da goyon bayan akalla 'yan majalisa 23. Dokar ta mayar da 'yan adawa saniyar ware. Shugaba mai ci Bashar al-Assad da ke mulki tun a shekarar 2000 shi ne zaim lashe zaben. Domin sauran 'yan takarar guda biyu ba sanannun mutane ba ne. Maher al-Hajar na jam'iyyar Kwaminisanci, dan majalisar dokoki ne sannan shi kuma Hassan al-Nuri dan kasuwa ne kuma tsohon wakili ne a majalisar dokoki.

Kamfen a kafofin yada labarun kasa

Yakin neman zabe ya fi gudana ta kafofin yada labaru na kurkusa da gwamnati. Shi ma shugaba Assad ya fi bayyana a gidan telebijin, inda aka fi ganisa yana ganawa da iyalai da kuma dangin sojojin Siriya da suka rasu a yakin basasar kasar.

Syrien Anschlag 33 Tote
Wata unguwa da yaki ya daidaita a SiriyaHoto: Zein Al-Rifai/AFP/Getty Images

Mazauna birnin Damaskus kamar wannan matar suna doki ga zaben.

"Ina yi ma kaina fatan samun wani shugaba dan kishin kasa da zai tabbatar da tsaro a Siriya tare da girmama dokokin kasa. Domin Siriya ta mu ce mu duka."

Shugaban hukumar zaben Siriya ya ba da tabbacin cewa hukumar mai zaman kanta ne kuma ba za ta fifita wani dan takara a kan wani ba.

Zabe cikin yanayin yaki

Shekaru uku kenan da fara boren kyamar gwamnati wanda ya rikide zuwa yakin basa, abin da ke saka ayar tambaya ga yadda za a iya gudanar da zabe a cikin wannan yanayi, inda kuma alkalumma suka nuna cewa fiye da kashi 40 cikin 100 na 'yan kasar sun yi gudun hijira.

Libanon Syrien syrischer Flüchtlinge wählen in Beirut Präsidentschaftswahl von Bashar al-Assad
'Yan gudun hijirar Siriya ke zabe a LibanonHoto: JOSEPH EID/AFP/Getty Images

To sai dai Bashar Yousef dan jarida ya ce 'yan Siriya za su kada kuri'a a yankunan da ke karkashin ikon gwamnati.

"Ina jin zaben zai gudana kamar yadda aka saba gabanin barkewar rikicin a Siriya. Dalibai da ma'aikatan gwamnati na da muhimmanci ga zaben, saboda haka za a tilasta musu zuwa rumfunan zabe. Da yawa daga cikin 'yan kasar za su kada kuri'a saboda tsoron ka da hukumomin su hukunta su idan ba su sauke wannan nauyi ba."

'Yan adawar kasar ta Sriya dai sun kaurace wa zaben da suka kira wani wasan kwaikwayo da zai biya bukatun shugaba Assad na ci gaba da shugabancin kasar.

Mawallafa: Mona Naggar / Mohammad Nasiru Awal
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe