1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mali ta gudanar da zabe

Usman Shehu Usman
April 19, 2020

A wannan Lahadi kasar Mali ta gudanar zaben 'yan majalisar dokoki zagaye na biyu wanda masu aiko da rahotanni ke cewa zaben ya gudana karkashin matsalolin tsaro.

https://p.dw.com/p/3b9Ip
Mali Wahlen 2020
Hoto: imago images/Afrikimages/A. Keita

Babba misali na rashin tsaro, a wasu mazabun ala tilasr hukumar zabe ta canza wasu wuraren kada kuri'a na rumfuna, domin an yi ta samun hare-haren 'yan bindiga da ke ikirarin jihadi. Dama dai jama'a sun yi ta nuna shakkun gudanar da zaben musamman a arewaci da tsakiyar kasar ta Mali, inda 'yan ta adda ke kai wa jami'an gwamnati da fararen hula hari. To amma bisa dagewar da gwamnati Ibrahim Boubakar Keita, an ci gaba da zabe, amma a wannan zagaye na biyu an samu karancin fitowar jama'a. Baya ga matsalar tsaro, akwai kuma annobar Coronavirus wanda yanzu haka ke yaduwa a kasar ta Mali. Bisa matsalolin tsaro, wasu daga cikin 'yan takaran ba su samu ko daman yin yakin neman zabe ba. Shi kansa babban jagoran adawan kasar ta Mali Soumaila Cisse, wasu da ba'a kai ga sanin ko su waye ba, sun sace shi gabanin gudanar da zaben.