Zabe a kasar Bama | Labarai | DW | 07.11.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zabe a kasar Bama

Kasar Bama ta shirya zaben farko a cikin shekaru 20, saidai adawa ta kaurace

default

Aung San Suu Kyi shugabar adawa a Bama

A kasar Bama,an fara kada kuri´ar zaben yan majalisun dokoki, a cikin tsatsauran matakin tsaro.

Kimanin mutane miliyan 30 ne ya cencenta su kada kuri´a, a wannan zabe irin sa na farko a cikin shekaru 20 da su ka gabata.Saidai sojojin da ke rike da ragamar mulki a kasar, sun haramtawa Aung San Suu Kyi ,shugabar yan adawa shiga wannan zabe.

Kuma babbar jam´iyar adawa ta yi kira ga magoya bayanta, su kauracewa zaben.

Kasashen Faransa, Britaniya, da Italiya, sun yi hannunka mai sanda, ga turawan da ke bukata zuwa Birma a cikin yan kwanakin nan , saboda hasashen gurbacewar harakokin tsaro.

Wannan kasa dai na cikin mulkin soja, tun shekara 1962.

Tunni dai Kasashen yammacin duniya sun bayyana kin amincewa da sakamakon zaben, wanda a cewar ba zabe ne ba na demokradiya.

Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi

Edita: Ahmad Tijani Lawal