Za′a je zagaye na biyu a zaben kasar Benin | Labarai | DW | 08.03.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za'a je zagaye na biyu a zaben kasar Benin

Hukumar zaben kasar Benin CENA ta bada samakon karshe na zaben shugaban kasa, inda Lionel Zinsou zai fafata da Patrice Talon a zagaye na biyu.

Benin Präsidentschaftskandidat Lionel Zinsou nach der Stimmabgabe

Lionel Zinsou

Sakamakon da hukamar zaben kasar ta Benin dai ta CENA ta bayar ya nunar cewa Firaminista Lionel Zinsou ne ke kan gaba da kashi 28,44 cikin 100 yayin da Patrice Talon ke bi masa da kashi 24,80 cikin 100, sai na uku Sebastien Ajavon wanda ya samu kashi 23,03 cikin 100 kamar yadda shugaban humar Emmanuel Tiando ya sanar a gaban manema labarai. Kotun tsarin mulkin kasar ce dai ke da nauyin tantance wannan sakamako sannan ta fitar da sakamako na dindindin.

Shugaban kasar ta Benin mai barin gado Docta Thomas Boni Yayi, bai nemi sake tsayawa takara ba, bayan da ya kammala wa'a din mulkinsa na biyu, abun da ya sa ake yi wa wannan karamar kasa ta Yammacin Afirka kallon wata abun musali a fagen demokaradiyya. 'Yan takara 33 ne dai da ke neman shugabancin kasar suka fafata.