Za je zagaye na biyu a zeɓen Mali
November 28, 2013Talla
Hukumar ta ce ya zama dole a gudanar da zagaye na biyu na zaɓen 'yan majalisun dokokin ranar 15 ga watan Disamba da ke tafe. Daga cikin kujeru 147 da aka ware a majalisar dokokin, kujeru 16 kawai jam'iyyun siyasar da suka yi takara suka samu.
Wadanda suka haɗa da jam'iyyar shugaban ƙasar Ibrahim Boubacar Keita wato RPM wacce ta sami kujeru guda takwas,da jam'iyyar Soumaila Cisse ta URD da ta samu kujeru biyar yayin da ADEMA ta ke da kujeru guda biyu.Hukumomin ƙasar ta Mali dai sun ce jama'a ba su fito ba a zaɓen.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Umaru Aliyu