Za a yi gasar CAF a Equatorial Guinea | Labarai | DW | 14.11.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a yi gasar CAF a Equatorial Guinea

CAF ta bai wa Equatorial Guinea ragamar shirya gasar cin kofin ƙwallon ƙafa na Afirka wanda za a yi a cikin watan Janairu.

Hukumar ƙwallon kafa ta nahiyar Afirka CAF ta bayyana ƙasar Equatorial Guinea, a matayin wadda za ta karɓi baƙwancin gasar cin kofin ƙwallon kafa na nahiyar a cikin sabuwar shekara mai shirin kamawa wacce za a soma a ranar 17 ga watan Janairun da ke tafe.

Hukumar ta ce ƙasar ta Equotorial Guinea za ta shiga gasar kai tsaye ,ba tare da shiga gasar share fage ba ta takande da rairaiyi na wasannin.Wannan zaɓi,ya biyo bayan da ƙasar Maroko wacce aka shirya tun farko za ta shirya gasar ta janye saboda tsoron jin bazuwar cutar Ebola a ƙasarta.