Za a tattara kuɗaden taimaka wa al′ummar Gaza | Labarai | DW | 09.09.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a tattara kuɗaden taimaka wa al'ummar Gaza

Falasɗinu da Majalisar Ɗinkin Duniya sun ƙaddamar da wata gidauniya domin tattara kuɗaɗe akalla miliyan 427 na Euro saboda al'ummar Gaza.

Za a tattara kuɗaɗen ne da nufin kai agajin jin ƙai na gaggawa ga dubban fararar hula, waɗanda yaƙin na Gaza ya taggayara, gabannin taron ƙasashen duniya masu hannu da shuni da za a yi a cikin watan Okotoba a kan yankin na Gaza.

Yaƙin na Gaza wanda aka kwashe kusan tsawon wata guda ana yi,ya yi sanadiyyar mutuwar mutane sama da dubu biyu tare da lalata gidaje kusan dubu 40 da kuma cibiyoyin samar da ruwan sha da wutar lantarki.

Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Pinado Abdu Waba