Za a sake zaben shugaban Ostiriya | Labarai | DW | 05.07.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a sake zaben shugaban Ostiriya

Gwamnatin Ostiriya ta saka lokacin zaben bayan kotun tsarin mulki ta soke sakamakon zaben da ya gabata saboda takaddama kan wasu makudan kuri'u.

Za a sake gudanar da zaben shugaban kasar Ostiriya ranar 2 ga watan Oktoba mai zuwa, bayan soke sakamakon zaben da ya gabata. A wancan zaben Alexender Van der Bellen ya samu nasara da karamin rinjaye a kan mai ra'ayin kyamar baki Norbert Hofer.

Gwamnatin kasar ta bayyana soke sakamakon zaben da kuma saka sabon lokacin da za a sake. Kotun tsarin mulki wadda ta soke zabe ta ce akwai takaddama kan kimanin kuri'u 80,000, kuma dama da kuri'u 31,000 Van der Bellen masanin tattalin arziki ya samu nasarar zaben da ya gabata.

A watan Oktoba mai zuwa za a sake fafatawa tsakanin 'yan takaran biyu Van der Bellen dan shekaru 72 da haihuwa da kuma Hofer dan shekaru 45, domin sanin wanda zai zama shugaban kasar ta Ostiriya na gaba.