Za a sake gudanar da wasu zabubbukan majalisun kasar Haiti | Labarai | DW | 21.08.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a sake gudanar da wasu zabubbukan majalisun kasar Haiti

Jami'an hukumar zaben kasar Haiti sun tabbatar da cewa akwai wuraren da za sake zabukan 'yan majalisu.

Hukumar zabe ta wucin gadi a kasar Haiti ta ce za a sake gudanar da wasu zabubbukan 'yan majalisu a kusan gundumomin zabe guda biyar da aka samu karancin futowar masu kada kuri`a da a kalla kashi 18 cikin dari.

Hukumar zaben dai taba sanarwar sake zabubbukan ne a wata ganawa da ta yi da manema labarai ne birnin Port AU Prince.

Jami'an hukumar zaben su kace sun sanya sunayen wadanda suka samu nasara a kan shafin yanar gizon hukumar ga dukkanin wadanda suke muradin ganewa idanuwan su wadanda suka lashe zaben.

Sakamakon na nuni da cewar mataimakan majalisar uku ne aka zaba a cikin mutane 119 da suka tsaya takara kana kuma suna da mako daya kacal domin kalubalantar sakamakon zaben.

Kasar Haiti dai na fuskantar gibi na siyasa a yayin da take ci gaba da farfadowa daga barnar da girgizar kasa ta haifar a shekara ta 2010 a inda mutane sama da dubu 250 suka rigamu gidan gaskiya.