1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

ECOWAS za ta ladabtar da sojoji masu mulki a Guinea Conakry

Abdoulaye Mamane Amadou
September 23, 2022

Shugabannin kasashen Afirka membobin kungiyar ECOWAS/CEDEAO sun bayyana anniyarsu ta daukar matakan ladabtarwa ga jagororin gwamantin mulkin soja ta rikon kwaryar a Guinea Conakry.

https://p.dw.com/p/4HEzv
Ghana Accra | Economic Community of West African States | ECOWAS
Hoto: IVORY COAST PRESIDENTIAL PRESS SERVICE/REUTERS

Ecowas ta ce za ta cigaba da kakaba takunkuman ne sannu a hankali har sai an shimfida wani tsarin da ka iya mayar da kasar Guinea Conakry kan turbar dimukuradiyya, a yayin taron kolin da ta gudanar a wannan Alhamis a birnin New York.

Shugabannin kasashenn sun kuma yi kira ga gwamnatin mulkin sojan Mali da ta gaggauta sakin ragowar sojojin Côte d'Ivoire 46 da ta kama yau sama da makwanni ba tare da gindaya wani sharadi ba.

Ana sa ran a makon gobe wasu shugabannin kasashen memebobnin kungiyar ECOWAS/CEDEAO uku da suka hada da Ghana da Senegal da Togo, za su isa a Mali don lalubo mafita game da ragowar sojojin na Côte d'Ivoire 46 da fadar mulki ta birnin Bamako ta rike bisa tuhumasu da neman yi mata zagon kasa.