Za a janye dokar ta-baci da aka sa a Bangkok | Labarai | DW | 18.03.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a janye dokar ta-baci da aka sa a Bangkok

Gwamnatin Thailand ta ce za ta dage dokar ta-baci da ta sa a birnin Bangkok bayan yawaitar zanga-zangar masu kin jinin gwamnatin kasar da aka fuskanta a makonnin baya.

Mahukuntan kasar sun ce sun dau wannan mataki na janye wannan doka ce domin a halin yanzu kura ta fara lafa, sai dai za su yi amfani da wani tsari na tsaro da ake da shi dama can a birnin domin tabbatar da doka da oda, kuma wannan tsari zai fara aiki ne daga gobe Laraba zuwa 30 ga watan gobe.

A karshen watan Janairun da ya gabata ne dai gwamnatin ta Tahiland ta girka dokar ta baci domin dakile zanga-zangar da ta yi wa kasar dabaibaiyi, sai dai galibin abin da wannan doka ta kunsa ba su yi aiki ba musamman ma bayan da wata kotun kasar a tsakiyar watan da a gabata ta ce sanya dokar baya bisa ka'ida.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Usman Shehu Usman