Za a gudanar taro kan rikicin Myanmar | Labarai | DW | 30.03.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a gudanar taro kan rikicin Myanmar

Kungiyar kasashen Musulmai za ta yi taro bisa rikicin da ke faruwa a kasar Myanmar ko Burma

Kungiyar Hadin kan Musulmai ta bayyana a wannan Asabar cewa, ministoci daga Kungiyar Kasashen Musulmai na Duniya, za su gana ranar 14 ga wata mai kamawa na Afrilu a kasar Saudiya, domin tattaunawa kan rikicin da ke farauwa a kasar Mynmar ko Burma.

Sanarwar ta ce, za ayi ganawar a birnin Jeddah. Kafofin yada labaran kasar ta Myanmar sun bayyana karuwar mutanen da suka hallaka cikin rikicin na kwanaki 10, zuwa mutane 43, yayin da wasu 1300 suka rasa matsugunansu.

Mahukuntan kasar ta Myanmar sun bayyana daukan matakan da suka dace, domin dakile ruruwar rikicin tsakanin mabiya adddinin Budda da Musulmai.

mawallafi: Suleiman Babayo

Edita: Halima Balaraba Abbas