1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Za a gudanar da zabe a Guinea Bissau

June 28, 2013

Sama da shekara guda bayan juyin mulki a Guinea Bissau, gwamnati ta ce za a gudanar da zabukan kasar nan da watanni biyar.

https://p.dw.com/p/18yKL
Hoto: picture-alliance/abaca

Shugaban rikon kwarya na kasar Guinea Bissau Manuel Serifo Nhamadjo, ya bukaci a gudanar da zabe a kasar, batun da ya samu maraba daga kasashen nahiyar Afrika da kuma kasashen yamma.

Shugaba Manuel Serifo ya bayyana hakanne a wata sanarwa da aka karanta a gidan radiyon kasar, inda ya ce a yanzu kasar ta shirya gudanar da zabukan shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki da aka dakatar a baya, bayan tattaunawar da ya yi da sauran jamiyyun siyasar kasar kuma suka cimma matsaya.

Serifo ya bayyana cewa kawo yanzu an cimma dukkanin sharuddan gudanar da zabe mai inganci a kasar a watan Nuwamba mai zuwa.

Tun da farko dai an shirya gudanar da zabukan a watan Mayun da ya gabata kafin daga bisani a dage lokacin zaben.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Lateefa Mustapha Ja'afar