Za a fara sabon binciken jirgin Malesiya | Labarai | DW | 10.01.2018
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a fara sabon binciken jirgin Malesiya

Gwamnatin Malesiya ta sha alwashin ba da dala miliyan 70 ga wani kamfanin Amirka da ya kware wajen bincike a Teku don fara sabon bincike kan jirgin kasar samfurin MH370 da ya yi batan dabo shekaru hudu baya.

Ministan kula da sufurin kasar Malesiya Liow Tiong ya ce gwamnati za ta biya kudaden ne kawai idan har kamfanin ya gano akwatin nadar bayanan jirgin wato Black Box a ciki kwanaki 90.

Za a fara sabon binciken ne a tsakiyar watan Janairun shekarar 2018 a wurin da ya kai fadin murabba'in kilomita dubu 25,000 a kudancin Tekun Indiya.

Tun bayan batan jirgin a watan Maris din shekarar 2014 tare da fasinjoji sama da 200, an fara samun wasu tarkacen jirgin a sassan gaban tekun wasu kaashen Afirka.