Za a cigaba da shari′ar Assange a Birtaniya | Labarai | DW | 04.01.2021
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Za a cigaba da shari'ar Assange a Birtaniya

Hukumomin Amirka sun sha alwashi maido shari'ar mai shafukan WikiLeaks a kasar.

Wata kotu a Birtaniya ta yi watsi da bukatar Amirka, dangane da batun mika mata mutumin nan da ke bankado bayanan sirri tare da wallafa su a shafukan intanet na WikiLeaks. Sai dai Amirkar ta ce ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen ganin an hanna ta mutumin dan asalin kasar Ostireliyakuma a cewar hukumomin kasar ta Amirkar masu shigar da kararta sun shirya tsaf domin kalubalantar hukuncin kotun da ke birnin Landan.

Julian Assange mai shekaru 49 da haihuwa na fuskantar tuhume-tume 18, cikin su har'da na bankado bayanan sirrin hukumar sojojin Amirkar.