Zaɓen ′yan majalisun Dokoki a ƙasar Habasha | Labarai | DW | 24.05.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Zaɓen 'yan majalisun Dokoki a ƙasar Habasha

A wannan Lahadin ce 'yan ƙasar Habasha kasa ta biyu mafi yawan al'umma a Afirka , suke kaɗa ƙuri'unsu a zaɓen 'yan majalisun dokoki na ƙasa da na jihohi.

Sai dai abin kawai da ba'a sani ba, shi ne girman nasarar da gamayyar jam'iyyun da ke mulki tun daga shekara ta 1991 a ƙasar za su yi a wannan zaɓe, wanda kuma zai ba da damar sake mayar da Firaministan ƙasar Hailemariam Desalegn ga wani sabon wa'adin mulki.

Akalla dai 'yan ƙasar ta Habasha milian 36,8 ne za su zaɓi 'yan majalisun dokokin ƙasar da na jihohi a kalla 547 a zaɓen da ke a matsayin na farko tun bayan rasuwar shugaban ƙasar na wancan lokaci Meles Zenawi, wanda ya rasu sakamakon rashin lafiya a shekara ta 2012 bayan da ya shafe shekaru 20 a kan karagar mulkin ƙasar.