1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Versöhnungsversuche in der ZAR

February 18, 2014

Duk da cewa yawancin musulmin dake jamhuriyar Afirka ta Tsakiya sun tsere Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Turai na tallafawa wani shirin da zai daidaita tsakanin ɓangarorin

https://p.dw.com/p/1BBAp
Zentralafrikanische Republik Versuche der Versöhnung
Hoto: Bettina Rühl

A Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya rikicin na daɗa yin ƙamari, Kirista da Musulmi na cigaba da kashe juna, waɗanda suka kasance abokan arziƙi a baya ma sun zama maƙiyan juna, yawancin musulmin ƙasar sun tsere neman mafaka a ƙasashe maƙota, ga shi kuma dakarun Faransa da Afirkan dake wurin sun gaza kare fararen hula kamar yadda aka zata tun farko. To amma, duk da irin ƙiyayyar dake tsakanin ɓangarorin dake faɗa da juna, an ɗauki matakin farko wajen sassantawa.

A ƙarƙashin wata bishiya ne wasu maza da mata ke zaune suna tattaunawa da wani babban baƙon da suka samu, mai suna Abdou Dieng wanda Jami'i ne na hukumar ba da agaji ta Majalisar Ɗinkin Duniya dake Jamhuriyar Afirka ta Tsakiyar, kuma ya zauna ne yana sauraron ƙorafe-ƙorafen waɗannan mutane waɗanda mazauna babban birnin ƙasar ne wato Bangui.

Tattaunawar dai ta mayar da hankali ne kan girka kwamitoci ne na sassanntawa inda kawo yanzu an sami guda biyu, akwai wanda ke wakilcin mata da maza, tsoffi da matasa, sai kuma da wanda ke da wakilcin shugabanin ƙauyuka ƙungiyoyin agajin cikin gida, Kristoci da ƙungiyoyin matasa.

Zentralafrikanische Republik Versuche der Versöhnung
Ɗaya daga cikin mayaƙan anti balakaHoto: Bettina Rühl

Kwamitocin wakilan Al'umma

Kwamitocin na cigaba da tattaunawarsu inda suke la'akari da yawan yankunan dake cikin birnin, amma kuma kamar sun yi tuya sun mance da albasa tunda rukuni ɗaya mai mahimmanci wato ɓangaren musulmi a ƙasar ba shi da wakilci cikin kwamitocin domin duk sun gudu. Kuma yana ɗaya daga cikin dalilan da ya kawo Abdou Dieng domin ya jagoranci shirin sulhu na musamman wanda ke samun tallafin Majalisar Ɗinkin Duniya da Ƙungiyar Tarayyar Turai

"Idan babu musulmi a cikin wannan yankin, kuma kafin ɓarkewar rikicin an tabbatar cewa akwai wasunsu da suka zauna a nan, wajibi ne ku koyi yadda zaku zauna tare, ba dole sai addinin ku ɗaya ba, abubuwan da suka banbanta mutane ma ai suna da amfani, ana iya samun addinai daban-daban, banbanci a launin fata, banbanci a yanayin tunani amma kuma a kasance ana ma'amala da juna cikin mutunci. Dukkanku al'umma ɗaya ce a ƙasa guda babu rukunin da ya fi wani 'yancin zama a wannan ƙasar. Wajibi ne ku koyi, zama da banbance-banbance domin ku yi amfani da dammakin da kuke da su"

Matakin horas da al'umma

Al'ummar Afirka ta tsakiya ta dare gida biyu kuma ko ta halin ƙaƙa ya kamata a samu a sulhunta tsakaninsu duk da irin ƙalubalen da zaa fiskanta wajen yin haka, Kwamitocin biyu da aka kafa suna gudanar da wata horaswa na wuni biyu kuma Jose Carlos Rodriguez na ɗaya daga cikin masu ba da horon wanda ya ce a jiya sun tattauna batun rikicin yau kuma suna tattauna batun sulhu kuma ya ce ya san dukkansu na cikin yanayi na ɗimuwa da tashin hankali

"Abin da ya fi bani wahala a yanzu haka shi ne tashi kowani safe in bar gida, kuma a yayin da nake tafiya in riƙa jin harebuin bindiga amma kuma in jajjirce in tafi wurin aiki, ba tare da sannin abin da zai faru ba, wannan na nufin rashin tsaron ya shafi dukanmu ne, muna cikin fargaba, ba zan ɓoye irin tsoron da nake ji ba na yi shekaru 20 ina aiki a wuraren dake fama da rikici amma ban taɓa zama wurin ba."

Wannan yanayi dai shi ne kusan kowa ke fama da shi, kamar dai Zara Sonja Holona mai shekaru 35 na haihuwa wanda komai ya faru a idonta, ta ga yadda aka riƙa kwasar ganima, aka riƙa kashe waɗanda ba su ji ba su gani ba, amma kuma duk da haka, tana ganin mahimmancin hawa kan teburin tattaunawa, amma kuma ta san cewa domin hakan ya yi nasara suna buƙatar taimako

Zentralafrikanische Republik Versuche der Versöhnung
Illar rikici a kan yara tun ba su kai ko'ina baHoto: Bettina Rühl

"Ƙiyayya ne a zukatanmu, tsana ya riga ya ci cikin zukatanmu, amma ina fata wannan horaswar da ake mana zai taimake mu har mu koyi yadda zamu yi nasara kan ƙiyayyar da ya riƙe mu haka"

Duk da wannan yunƙuri na tattaunawa akwai waɗanda ke fargabar zuwa inda ba su da rinjaye domin gudun shiga hannun waɗanda ka iya yi musu illa

Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar