1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunwa na barazanar halaka dubban yara a Kongo

Ramatu Garba Baba
December 12, 2017

Asusun kula da yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce yara dubu dari hudu 'yan kasa da shekaru biyar a Jamhuriyar Kongo na fama da tsanani na rashin abinci mai gina jiki da ke barazana ga rayuwarsu.

https://p.dw.com/p/2pFAB
Angola flüchtchtlings Kinder aus Kongo
Hoto: UNICEF/N. Wieland

Yaran da ke a yankin Kasai da rikici na fiye da shekara guda ya daidaita ne ke bukatar taimako wanda idan ba a dauki mataki na magance matsalar cikin gaggawa ba, za iya kai wa ga mutuwar yara akalla  dubu dari hudu acewar asusun da ke kula da yara, karancin anfani gona da daruruwan jama'a da suka rasa matsuguni a sanadiyar rikicin shi ya jefa yaran cikin wannan hali. Alkaluma na nuni da cewa, asibitoci da dakunan shan maguguna akalla dari biyu da ashirin aka lalata a yayin rikicin yankin na Kasai, mutane fiye da dubu uku aka tabbatar da cewa sun mutu a tashin hankalin.