1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Fargabar yunwa a Arewa maso Gabashin Najeriya

Abdullahi Tanko Bala RGB
May 18, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana fargabar kan barazanar yunwa a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya. Majalisar na fuskantar karancin kudadden gudanar da ayyukan jin kai.

https://p.dw.com/p/4RYDY
Rikicin Boko Haram ya sa miliyoyi na fuskantar barazanar yunwa
Rikicin Boko Haram ya sa miliyoyi na fuskantar barazanar yunwaHoto: Katerrina Vittozzi/Unicef/picture alliance

Ofishin kula da ayyukan jin kai na Majalisar Dinkin Duniya ya kadammar da shirin samar da kudadde don gudanar da ayyukan jin kai ga mutanen da ke fama da karancin abinci mai gina jiki, saboda  barazanar yunwa a jihohin Borno da Adamawa da kuma Yobe. Majalisar tana fuskantar gibin kudin da take bukata da ke barazana ga ayyukanta.

Kadammar da wannan shiri da ofishin kula da ayyukan jin kai na majalisar ya yi, ya janyo hankali ne a kan karancin kudadden gudanar da ayyukanta a Najeriya wanda ta ce, ya zuwa yanzu kashi 15 cikin 100 na yawan kudadden ne ta samu, abin da ke daga hankali sosai. Domin a yanzu hukumar ta ce, mutane milyan 2.8 mafi yawansu mata da yara kanana a wadannan jihohi na Borno da Yobe da Adamawa ne ke fuskantar barazanar yunwa da karancin abinci mai gina jiki.

Yan gudun hijirar Maiduguri
Yan gudun hijirar MaiduguriHoto: imago/epd/A. Staeritz

Tun daga 2020 ne dai ake fuskantar raguwar kudadden da ake gudanar da ayyukan jin kai a yankin Arewa maso Gabashin Najeriyar, lamarin yafi muni a lokacin damina, domin akwai wuraren da ba’a iya kai wa gare su saboda matsala ta rashin tsaro da damina. Abin da ya fi daga hankali shi ne, mata masu ciki da shayarwa sun kai dubu 179 da ke fuskantar wannan mumunan hali.

Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na fuskantar barazanar yunwa
Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya na fuskantar barazanar yunwaHoto: picture-alliance/dpa/Gilbertson

Kungiyoyin farar hula da jakadun kasashen duniya sun hallarci kadammar da wannan shiri don janyo hankalin kasashen duniya a kan wannan lamari, domin a lokacin damina baya ga karancin abinci ana fusknatar karancin ruwan sha da bullar cututtuka ga mutanen da ke dogaro a kan tallafin. 

Yakin da ake yi Ukraine da na Sudan ya sanya hankalin kasashen da ke bayar da taimako karkata zuwa can. A yayin da ake neman tallafi daga kasashen duniya a kan wannan lamari, kwararru na bayyana bukatar tsara mafita daga Najeriya da za ta kasance abin dogara da kuma kula da mutanen da ke fama da karancin abinci.