Yunkurin zaman lafiya a Kongo | Labarai | DW | 01.12.2012
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin zaman lafiya a Kongo

'Yan tawayen M23 sun fara janyewa daga garin Goma da suka kwace daga dakarun gwamnatin Kongo.

'Yan tawayen M23 da suka kwace iko da garin Goma na hamhuriyyar Doimokradiyyar Kongo tun a ranar 20 ga watan Nuwamban nan, sun fara janyewa daga garin suna yin wake-wake da wasa da makamai a wannan Asabar. Wannan matakin da suka dauka dai ya karfafa fatan kokarin samar da zaman lafiya da kuma tattaunawar kawo karshen rigingimun da yankin ya fada ciki a baya bayannan.

Kimanin mako guda kenan da shugaban Uganda, dake zama shugaban kungiyar kasashen yankin Great Lakes ya jagoranci wani shirin sulhu, wanda a lokacin ne kuma ya bukaci 'yan tawayen su janye daga birnin na Goma bayan da suka fatattaki sojojin gwamnatin jamhuriyyar Dimokradiyyar Kongo da ke samun goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya. A da dai 'yan tawayen sun sha alwashin kifar da gwamnatin shugaba Josef Kabila, wadda ke da hadikwata a birnin Kinshasa.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Yahouza Sadissou