Yunkurin warware rikicin Ukraine da Rasha | Labarai | DW | 09.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin warware rikicin Ukraine da Rasha

A karon farko, bangarori hudu sun amince da tattauna rikicin kasar Ukraine a mako mai zuwa. Amirka na zargin Rasha da ingiza rikicin yankin gabashin Ukraine.

Jami'ar kula da harkokin ketare ta EU Catherine Ashton za ta hade da ministocin harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov da takwaransa na Ukraine Andriy Deshchytsia da sakataren waje na Amirka John Kerry.

Kerry dai ya zargi dakarun Rasha da ingiza wutar rikicin yankin gabashin Ukraine, inda masu goyon bayan Moscow dauke da makamai ke ci gaba da mamaye gine-ginen gwamnati a birane biyu. Tun ranar Lahadi ce dai, masu zanga-zangar suka karbe madafun ikon gine-ginen inda suke bayyana muradin ballewa daga kasar ta Ukraine. Rasha dai ba ta yarda da halalcin gwamnatin Kiev da aka nada a watan Fabrairu ba, bayan hambarar da gwamnatin shugaba Viktor Yanukovych. Kerry ya fada wa majalisar Amirka cewar Rasha na biyan wasu domin su wargaza kasar ta Ukraine.

"A bayyane take cewar sojojin Rasha na musamman da wakilanta ne ke da alhakin tashe-tashen hankulan da ke gudana.Tuni aka cafke wasu. Kuma yana da muhimmanci a san cewar Amirka da kawayenta ba za su ji nauyin amfani da matakan karni na 21, domin hukunta Rasha da ke nuna halin karni na 19 ba".

To sai dai sabanin abun da Amirka ke ikirari, wakilin DW da ke birnin na Donetsk Markus Reher, ya ce babu wata shaida da ke tabbatar da cewar Rasha na da hannu a ringingimun da ke gudana a yankin.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Mohammad Nasiru Awal