1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin wanzar da zaman lafiya a Filato

Abdullahi Maidawa Kurgwi/ASJune 3, 2015

Shugabanin addinai a jihar Filato da ke tsakiyar Najeriya sun kawo shawar yadda gwamnatin jihar za ta kyautata zaman lafiya tsakanin mabiya addinai don gujewa samun rikici.

https://p.dw.com/p/1FbAh
Interfaith Mediation Centre in Kaduna
Hoto: Katrin Gänsler

A shekarun baya dai jihar Filato ta tsinci kanta cikin rigingumu da ke da nasaba da kabilanci da addini, lamarin da ya janyo zaman gaba tsakanin al'ummomi daban-daban. To sai dai kuma bayan da aka samu sauyin gwamnati a jihar, akwai alamun cewar yanzu hankulan jama'a sun soma koma jikinsu duk kuwa da kasancewar ana samun kai hare-hare da sace-sacen shanu nan da can.

Wannan yanayi da ake ciki ne dai ya sanya shugaban kungiyar matasan Kirista shiyyar jihohin arewa maso tsakiya Injiniya Daniel Kazai, ya kawo shawara ga sabuwar gwamnatin Filato cewar kada ta maimaita wasu abubuwan da tsohuwar gwamnatin jihar ta Jonah Jang ta aikata. Shi kuwa Malam Mohammad Harrisu Abubakar wani fittacen malamain addinin Musulunci a jihar Filato, ya ce tun a baya wasu shugabanin jihar ne ke haddasa rikicin don biyan bukatu na kashin kansu.

Masharhanta dai sun lura cewar muddin gwamnatin jiha ko ta tarayya na son zaman lafiya tsakanin jama'ar ta, to za a samu hakan, kazalika idan ta kudiri aniyar kunna wutar rikici tsakanin jama'a to babu makawa sai ta yi. Wata matsalar da ke janyo tashin hankali dai itace rashin aikin yi dama talauci. Yanzu haka dai ana ta kiraye-kiraye na ganin an magance wannan batu, inda wasu ke neman gwamnatoci su yi mulki na adalci don dorewar zaman lafiya.

Nigeria Flüchtlinge wegen der Offensive gegen Boko Haram
Rigingimun addini na haifar da samuwar 'yan gudun hijira da ke ficewa daga yankunan da ake rikici don tsira da rai.Hoto: Reuters/A. Sotunde
Nigeria Bombenexplosion in Dukku Bus Rang in Gombe
A kan samu asarar dukiya da ta rai a lokutan da ake yin rikicin addini ko na kabila a Najeriya.Hoto: picture-alliance/dpa