Yunkurin samar da zaman lafiya a Mali | Siyasa | DW | 27.03.2017
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunkurin samar da zaman lafiya a Mali

An bude babban taron hadin kan kasa, inda ake sa rai wakilai 300 za su hallara, sai dai a arewacin kasar inda makomar yankin ke a sahun gaba a jadawalin taron, ba a tsammanin taron zai haifar da wani abin a zo a gani,

A duk rana matasa kan hadun a harabar wani gida da ke a tsakiyar birnin Gao da ke arewacin Mali don tattauna batutuwan da ke ci musu tuwo a kwarya. Issa Boncana guda ne a cikin matasan, memba ne kuma na wata kungiyar farar hula wadda aka kafa lokacin rikicin yankin a shekarar 2012. Maimakon su tsere, matasan sun rika kula da al'umma suna amfani da hanyoyin lumana wajen kushe masu tsauttsauran ra'ayi da suka mamaye yankin da ma kungiyoyin 'yan fashi. Ya ce yanzu haka harabar gidan ta kasance wurin haduwar matasan da ranar tsaka.

Ya ce: "A nan ba bu aikin yi. Ba masana'antu, kana ba a kula da batutuwan da suka fi ci wa matasan tuwo a kwarya. Ba mai samun aikin yi. A kullum muna zuwa nan wurin. Muna fata gwamnati za ta ji koke-kokenmu ta kirkiro mana da aikin yi. Amma yanzu kam babu komai a nan."

Tun gabanin barkewar rikici a arewacin Mali a karshen 2011 inda aka fara da tawayen Abzinawa sannan rikicin ya kaikololuwa sakamakon mamayar da kungiyoyin Islama suka yi, harkar yawon bude ido ta ruguje. Har yau ba a zuba jari  a yanki saboda dalilai na tabarbarewar tsaro. Moussa Souma Maiga shugaban al'umma ne a Gao.

Ya ce: "A bayyane yake, babu tsaro ko na miskala zarratin a wannan yanki. Ba ma iya fita yadda muke so, kusan muna cikin kurkuku ne. Komai ya sukurkuce."

A Gao inda aka girke sojojin Jamus da ke aiki karkashin rundunar MDD ta MINUSMA, sojojin kasa da kasa na sintiri a kan titunan tsakiyar birnin. Sai dai da zaran mutum ya fita daga yankin, to batun tsaro ya kare. A halin yanzu ma ana yada jita-jita cewa akwai wasu masu ikirarin jihadi a birnin.

A shekarar 2015 gwamnatin Mali da wsu kungiyoyin 'yan tawayen Abzinawa sun kulla yarjejeniya da ake aiwatar da ka'idojinta daki daki. Kuma a wannan Litinin za a shiga mataki na gaba, a babban taron hadin kan kasar a birnin Bamako da zai samu halarcin wakilan gwamnati da na 'yan adawa da kum tsoffin 'yan tawaye. Sai dai Issa Boncana matashi a Gao ba shakku game da samun nasara a taron.

Ya ce: "Ba a gaiyace mu da ma wasu kungiyoyin matasa a wannan babban taro ba. Ba wanda ya tuntube mu. Idan aka samu maslaha, to masala ce ta Bamako, amma ba ta Mali ko arewacin kasar ba."

Sai dai shugaban al'umma Moussa Souma Maiga na da kyakkyawan fata game da muhimmacin taron, amma ya yi kira da a yi takatsantsan. Ba wanda zai iya sanin ko a karshen taron a ranar 2 ga watan Afrilu za a samu wata kwakkwarar matsaya ga birnin Gao.