Yunkurin kasashen Turai kan Ebola ya zo a makare | Afirka a Jaridun Jamus | DW | 24.10.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Afirka a Jaridun Jamus

Yunkurin kasashen Turai kan Ebola ya zo a makare

Halin da ake ciki a Jamhuriyar Dimokradiyar Kwango da batun Boko Haram a Najeriya da yaki da cutar Ebola sun dauki hankalin jaridun Jamus a wannan mako.

Jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung tayi magana game da lambar yabo ta Sacharow da aka baiwa wani likitan mata na kasar ta Kwango, mai suna Denis Mukwege, saboda taimako da gudummuwarsa ga kula da lafiyar matan kasar da aka ci mutncinsu ta hanyar fyade, musamman daga kungiyoyin yan tawaye, ko kamar yadda ake zargi, daga sojojin rundunar kiyaye zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya. Jaridar tace Mukwege ya zama wata alama ta fata da ceto ga matan na Kwango, wanda ma saboda kyakkyawan aikinsa ne a asibitin Panzi dake Bukavu a gabashin Kivu, ya sanya aka bashi lambar yabon ta Sacharow ta majalisar kasashen Turai.

Jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan mako tayi sharhi ne a game da hukuncin da wata kotu a Afirka Ta Kuduta yankewa sanannen magujin nan na nakasassu, Oscar Pistorius, wanda a bayan shari'ar misalin watanni bakwai, a farkon wannan mako alkali Thokozile Masipa ta yanke masa hukuncin daurin shekaru biyar a gidan kaso, saboda laifin kisan budurwarsa, Reeva Steenkampf a bara. Jaridar Neue Zürcher Zeitung tace ra'ayoyi sun banbanta a game da wannan hukunci. Yayin da yan kasar da masana shari'a suke muhawara a game da sassaucin wannan hukunci, dangin Pistorius sun sanar da cewar ba za su daukaka kara ba. Pistorius idan har ya nuna halaye na-gari a lokacin zamansa a gidan kaso, ana iya yi masa sassauci, ya fito daga kurkukun tun a watan Agusta na shekara ta 2015, tare da dauki talala.

Jaridar Berliner Zeitung ita kuwa tayi magana ne kan gwagwarmayar yaki da cutar Ebola. Tace ganin yadda a wannan mako, kasashn Turai suka tashi tsaye domin hada gwiwar ba da gudummuwar yaki da cutar da ta addabi yankin Afirka ta yamma, wannan mataki na su ya zo a makare. Tun a watan Disamba na bara ne kasar Guinea ta sanar da fara bullar cutar ta Ebola, sa'annan a watan Maris, aka kwatanta wannan cuta a matsayin annoba, yayin da cikin watan Yuli, Peter Piot na CNN yayi gargadi a game da mamayewar da Ebola din ta yiwa kasashen Afrika ta yamma uku, wato Guinea da Saliyo da Liberiya. Duk da haka ba'a dauki wani mataki ba, inda suma kasashen Turai sai a ranar Litinin suka daidaita a game da nada wakilinsu na musamman da zai kula da matakan da zasu dauka na yaki da cutar.

Anschlag in Maiduguri Nigeria Archiv Juli 2014

Alamun hare-haren Boko Haram a Najeriya

Najeriya ta ce ta cimma yarjejeniyar tsagaita bude wuta da yan kungiyar Boko Haram. Jaridar Tageszeitung a sharhinta, tayi tambayar: shin da wace kungiya Najeriya ta cimma yarjejeniyar a zahiri. Wannan tambaya ta dace, inji jaridar, domin kuwa idan har akwai yarjejeniyar, me ya sanya ake ci gaba da samun tashin hankali da kashe-kashe da sace yan mata har yanzu? Jaridar tace ya zuwa yanzu dai babu wanda yake da masaniya a game da wannan yarjejeniya tsakanin gwamnati da yan Boko Haram, wadda aka ce an kai gareta ne bayan tattauna a Chadi, karkashin shugaban kasar Idriss Deby, kuma a karkashinta yan kungiyar ta Boko Haram zasu saki yan matan Chibok fiye da 200 da suka kama tsawon fiye da watanni shidda, kuma har yanzu suke tsare a hannunsu. A daura da haka ma, kungiyar ta ci gaba da kai hare-haren bama-bamai da kone kauyuka da sace yan mata. Saboda haka ne jaridar Tageszeitung tace wannan yarjejeniya da babu wanda ya san irinta, bata wuce ta mafarki kawai ba.