Yunkurin kafa gwamnatin kawance a Jamus | Labarai | DW | 16.10.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin kafa gwamnatin kawance a Jamus

Jam'iyyar The Greens ta yi watsi da ci gaba da tattauna batun shiga cikin gwamnatin kawancen da CDU za ta jagoranta.

Jam'iyyar the Greens, wadda ke fatutukar kare muhalli, ta sanar da yin watsi da tattaunawar da ke da nufin shiga cikin gwamnatin kawancen da jam'iyyar CDU ta shugabar gwamnati Angela Merkel za ta jagoranta. Bagarorin biyu dai, sun gana a wannan Talatar (15. 10. 13), inda taron na su ya tashi baram baram kimanin sa'oi shida bayan farashi. Sun gaza warware takaddamar da ke tsakaninsu ne dangane da batutuwan da suka hada da samar da sauye sauye game da haraji a kan masu arziki, da sha'anin inshorar kula da lafiya, da kuma mafi karancin albashin da ma'aikaci zai karba.

Jagorar jam'iyyar the Greens, Claudia Roth, na mai ra'ayin cewar, har yanzu za su mika batun shiga kawancen ne ga babban taron jam'iyyar. Abin da hakan ke nufi dai shi ne a yanzu , shugabar gwamnati Angela Merkel, za ta kafa gwamnatin kawance ne kawai tare da jam'iyyar Social Democrat, wadda suka shirya sake ganawa a wannan Alhamis (17. 10. 13). Kujeru biyar ne kachal suka hana Merkel samun rinjaye a majalisar dokokin kasar, bayan sanar da sakamakon zabe a watan jiya.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu