Yunkurin hari ga mabiya addinin koptik a Masar
January 7, 2013Rundunar tsaro ta kasar Masar,ta bada sanarwar gano wata makerkeshiyar yunkurin kai hari a wata cocin mabiya addinin koptik a daidai lokacin da suke shugulgulan bukukuwan kristimati a wannan Litanin Da sahin subahin din safiyar yau ne,wani ayarin sojoji da ke sintirin a garin Rafah da ke kan iyaka da yankin zirin Gaza,suka cafke wasu mutane guda hudu dauke da nakiyoyi shake a cikin mota. Tuni kuma aka mika mutanen ga jami'an 'yan sanda da ke ci-gaba da yi musu bincike. Ana dai saran mutanen da suka fito daga yankin Zirin Gazan,masu tsautsauran kishin islama ne. Ko a shekarar bara,wani makamancin hakan ya faru,inda wasu mutanen da ba a gano ko su wane ba,suka tada bom a wani ginin mabiya addinin koptik,inda a kala mutane 3 suka rasa rayukansu.
Mawallafi: Issoufou Mamane
Edita: Mahamadou Awal Balarabe