Hong Kong: Illolin rikici kan tattalin arziki
August 21, 2019Talla
Duk da wannan fafutukar da masu zanga-zangar na yankin Hong Kong ke yi don tilasta ma Chaina fita daga dukkan lamuran kasar, akasarin 'yan kasar ta Chaina ba su ma san me ke faruwa a yankin ba. Sai dai masana sun yi hasashe kan tasirin da rikicin zai iya yi ga sha'anin kasuwanci musanman a babban birnin kasar ta Shanghai.
Yanzu haka dai hukumomin kasar Chaina sun kwan da cewar rikicin da ke faruwa a Hong-Kong kan iya yin tasiri a birnin kasuwanci kamar Shanghai, suma mazauna birnin suna tsoron abin da ka iya faruwa a birninsu, in aka ci gaba da yi wa gwamnati tawaye a Hong-Kong. A yanzu dai gwamnatin Beijing na daukar duk matakai da suka dace na kawo karshen rikicin Hong-Kong da kuma hana shi bazuwa cikin kasarta.