Yunkurin hallaka Pervez Musharraf | Labarai | DW | 03.04.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin hallaka Pervez Musharraf

Wani bam ya tarwatse daura da jerin gwanon motocin da ke tafe da tsohon shugaban mulkin sojin Pakistan Janar Pervez Musharraf.

Lamarin dai kamar yadda wani jami'in rundunar 'yansandan kasar Muhammad Hayat ya shaida, ya faru ne lokacin da aka dauko tsohon shugaban kasar daga wani asibitin soji da ke Rawalpindi zuwa gidansa a Islamabad.

Mai magana da yawun Mr. Musharraf din Aasia Ishaq ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na AP cewar tsohon shugaban na cikin koshin lafiya kuma ba wanda ya jikkata ko asarar rai da aka samu.

Ya zuwa yanzu dai ba wata kungiya da ta yi ikirarin kai harin bam din, ko da dai lokacin da Musharraf din ya koma kasar a bara daga gudun hijirar da ya yi kungiyar nan ta Taliban ta lashi takobin ganin bayansa.

Mawallafi: Ahmed Salisu
Edita: Umaru Aliyu