Yunkurin hallaka Joachim Gauck | Labarai | DW | 19.04.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin hallaka Joachim Gauck

Jami'an tsaro a Jamus sun bankado wata wasika da aka aika wa shugaban kasar dauke da sinadarai.

BERLIN, GERMANY - FEBRUARY 22: German President Joachim Gauck gives his much anticipated speech on Europe at Bellevue Palace on February 22, 2013 in Berlin, Germany. In his speech Gauck emphasized modern Europe's inherent diversity and appealed to Great Britain to remain a member of the European Union. (Photo by Sean Gallup/Getty Images)

Joachim Gauck

Hukumomi a Kasar Jamus sun lalata wata wasika da aka aikewa shugaban Kasar da ake zargin tana dauke da abubuwa masu fashewa.

Mai magana da yawun Shugaban Jamus Joachim Gauck yace an samu wasikar ne yayin da ake gudanar da bincike kan wasikun da aka aiko masa ta Email, inda kwararrau suka lalata wasikar a wajen fadar Gwamnatin Kasar, inda yace haryanzu basu gano daga inda wasikar take ba.

Wani Jami'in 'yansanda masu binciken manyan laifufuka na Jamus ya tabbatar da cewa an lalata wata wasika da ake zargin tana dauke da abubuwa masu fashewa sai dai yace har yanzu suna gudanar da bincike don tabbatar da hakan.

Mawallafiya: Lateefa Mustapha Jaafar
Edita: Yahouza Sadissou Madobi