1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin gyaran fuska ga kundin tsarin milkin Najeriya

November 8, 2012

Tarin matsalolin siyasa na daga cikin abun da ya sa wasu wakilan majalisar dattawan tarayyar Najeriya ke bukatar sabon fasasli ga kundin tsarin milkin kasar.

https://p.dw.com/p/16fVE
Hoto: Katrin Gänsler

A wata dama da zata baiwa daukacin 'yan Najeriya musamman talakawan kasar damar tofa albarakacin bakinsu a gyaran tsarin mulkin kasar na 1999, majalisar wakilan Najeriyar ta kadammar da matakan da za'a bi wajen sauraren ra'ayoyin yan Najeriya, domin samar da ingantaccen tsarin mulki da ka iya dacewa da muraddun alumm,ar kasar. Daga Abuja Uwaisu Abubakar Idris ya aiko da wannan rahoton.

Dogon jiran da aka dade ana yi tare da ma kace nace a game da batun gyran tsarin mulkin Najeriyar ya kama hanyar zama zahiri, inda daga kadammar da shirin a yanzu za'a gudanar da tarurruka a mazabu 360 na Najeriyar domin jin ko me 'yan Najeriya ke so a gayara a sassa 43 na tsarin mulkin Najeriya da jama'a suka dade suna bayyana korafin lallai suna bukatar gyara.

Wahlen Nigeria Ergebnis
Hoto: AP

Wadanan sassa da suka dade suna haifar da kace nace a tsakanin alumma da suka hada da batun samar da 'yan sanda na jihohi, bada cikakken iko ga yankunan kanana hukumomi, da kariya ga gwamnonin da ma rabon arzikin kasa. To ko wane tsari majalisar ta shirya za'a biyo wajen aiwatar da shirin da za'a fara daga ranar asabar 10 ga watanan? Hon Ahmed Baba Kaita dan majalisar wakilan Najeriya ne daga jihar Katsina.

Majalisar wakilan Najeriyar da ita ce bisa radin kanta ta bullo da wannan tsari da a lokaci guda za'a gudanar da shirin jin ra'ayin jama'a a mazabu 360 maimakon a shiyoyi shida da a lokutan baya aka yi. Wannan tsari ne da ake hangen zai iya baiwa talakan Najeriyar damar daga 'yar yatsarsa da ke nuna 'yanci na demokradiya, abinda Dr Kabir Mato masanin siyasa da ke jami'ar Abuja ke ganin ko wane muhimmanci hakan keda shi ga dorewar demokradiyar?

Nigeria Militär Parade NO FLASH
Hoto: picture-alliance/dpa

Muhimmin lamari a kan wannan batu shine sashi na 9 na tsarin mulkin Najeriyar da ya baiwa majalisar 'yanci sake yiwa tsarin mulkin kasar fasali bai bada ikon yin kuri'ar raba gargadama a kan kowace doka ba, lamarin da ya sanya masu kiraye-kirayen yin hakan da ke nuna yunkurin suka tashi warwas. To sai dai duk abubuwan da za'a yo sai sun samu amincewar majalisun dokoki na jihohi abinda ke nuna sauran aiki a gaba, to amma Hon Baba Kaita ya bayana cewa.

Kundin tsarin mulkin Najeriyar na 1999 dai ya kasance dankali sha kushe saboda kalon da ake mishi na cewa sojoji ne suka tsara shi tare da dankawa mulkin demokradiyar kasar, abinda ya sanya a lokutan baya Farfesa Wole Soyinjka ya nufi kotu domin neman ta bashi izinin dakatar da tsarin mulkin kasar.

Mawallafa: Uwais Abubakar Idris / Issoufou Mamane
Edita :Mohamadou Awal Balarabe