Yunkurin girka rundunar sojojin ECOWAS | Labarai | DW | 05.06.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin girka rundunar sojojin ECOWAS

Shugabannin kungiyar kasashen Yammacin Afirka ta ECOWAS ko CEDEAO sun yi fata kan kafa rundunar hadin gwiwa domin yaki da ta'addanci da ke samun gindin zama a yankin.

Burkina Faso Senegals Präsident Macky Sall

Shugaban kasar Senegal Macky Sall

Cikin jawabin da ya yi ne dai a babban zaman taron kungiyar da ya gudana a birnin Dakar na kasar Senegal, Shugaban Senegal Macky Sall da ke a matsayin shugaban kungiyar a wannan lokaci, ya ce barazanar ta'addanci na zama wani babban kalubale ga yankin Yammacin Afirka. Inda ya ce ya kyautu su fuskanci lamarin ta hanyar sanya duk karfinsu bisa wani tsari na bai daya da zai kasance mai dore wa.

Hakan dai na zuwa ne bayan wani mumunan hari da 'yan kungiyar Boko Haram suka kai a garin Bosso na Jihar Diffa a Jamhuriyar Nijar, inda suka hallaka sojoji 32 tare da jikkata wasu 68 da yammacin ranar Juma'a.

An zabi sabon shugaban hukumar ta ECOWAS dan kasar Benin Marcel Alain de Souza, sannan kuma shugabannin sun zabi Shugabar Liberiya Ellen Johnson Sirleaf, a matsayin shugabar kungiyar ta ECOWAS ko CEDEAO wadda ta canji shugaba Macky Sall na kasar Senegal.