Yunkurin fasa gidan yarin Bangui ya gamu da cikas | Labarai | DW | 24.02.2014
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yunkurin fasa gidan yarin Bangui ya gamu da cikas

Dakarun tarayyar Afirka sun dakile yunkurin da Anti Balaka ta yi na kutsawa cikin gdan yari a Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya.

Dakarun kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa da ke Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya, sun yi nasarar wargaza wani yunkurin da shugabannin mayakan Kiristoci na kungiyar Anti Balaka suka yi, a wannan Lahadin (23. 02. 14), domin kutsawa cikin gidan yarin Bangui, babban birnin kasar, tare da tallafin shugaban kula da kayayyakin da ke gidan yarin.

Majiyoyi sun tabbatar da cewar, dakarun kasar Rwanda da ke aiki a karkashin rundunar kiyaye zaman lafiyar da Kungiyar Tarayyar Afirka ta tura kasar ne suka yi nasarar dakile wannan yunkurin, kamar yadda rundunar ta Afirka ta sanar - cikin wata sanarwar da ta fitar. Wani mazaunin yankin ya ce tsawon mintuna biyar ne aka yi suna jin harbe harben bindigogi, wanda suka sake ji bayan lafawa na dan lokaci, kafin daga baya kuma manyan tankunan yaki na dakarun wanzar da zaman lafiya suka kawo dauki, tare da yin sintiri a yankin.

Wasu shugabannin kungiyar mayakan Kiristoci ta Anti Balaka, sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewar, fursunonin da ke gidan yarin ne ke kokawa akan matsalar karancin abinci.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Mohammad Nasiru Awal