Yunkurin dara Ghana gida biyu ya sa kotu ta daure 'yan aware
March 7, 2024Wata kotu a Ghana ta yanke wa wasu mutane hudu da suka hada da dan sanda da soja hukuncin daurin shekaru biyar a gidan yari, saboda samun su da laifin jagorantar kungiyar 'yan aware ba bisa ka'ida ba. A yayin yanke hukunci a Accra, mai shari'a Mary Maame Ekueh Yanzuh ta ce "Wannan hukuncin ya zama gargadi mai karfi game da duk wani yunkuri na yin barazana ga zaman lafiyar kasar Ghana."
Karin bayani: Martani kan dokar hana auren jinsi a Ghana
Shi wanda ya kafa kungiyar Michael Koku Kwabla ya sha daurin shekaru biyar a wakafi da tarar dalar Amurka 940 (kusan Euro 860), yayin da sauran mambobin kungiyar Nene Kwaku da Emmanuel Afedo da Abednego Mawena aka yanke musu hukuncin daurin shekaru hudu a gidan yari kowannen su. tun a shekarar 2017 ne aka kama shugabannin 'yan aware a yankin kogin Volta da ya kunshi kabilu da yawa, saboda haka ne suke so su mayar da yankin ya zama kasa mai cin gashin kanta.