Yunƙurin sasanta rikicin gwamnoni | Siyasa | DW | 27.06.2013
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Yunƙurin sasanta rikicin gwamnoni

Ƙungiyar gwamnonin Najeriya ta fara shirin magance rarrabuwar kawuna da ke cikinta

Treffen nigerianischer Gouverneure. Foto: DW-Korrespondent Ubale Musa, 26.6.2013 in Abuja

Taron gwamnonin najeriya

An dai kai ga kallon-kallo har an ma kai ga shagube a tsakanin gwamnonin tarrayar Najeriya dake rabe a gida biyu da kuma a karon farko suka kai ga hadin fuska dama goga kafada da junansu. To sai dai kuma sun kare da raha dama kokari na danne bambancin da ya tada hankali kuma ke kara fitowa fili da rikicin dake cikin kungiyar gwamnonin kasar mafi tasiri.

A cikin watan Mayun jiya ne dai aka wayi gari da zaben da ya kai ga samar da bangarori biyu na gwamnonin dake ikirarin shugabancin kungiyar mafi tasiri a siyasa. Zaben kuma da ya bar baya da kura ya kai har ga dakatar da akalla gwamnoni biyu cikin gwamnonin jamiyyar PDP 23, sannan kuma ya kai ga ruda daukacin harkoki na jamiyyar kasar mai mulki.

Nigerian President Goodluck Jonathan waves as he arrives to attend the funeral service for writer Chinua Achebe at Ogidi in southeast Nigeria on May 23, 2013. Renowned author Professor Chinua Achebe was buried at his Ogidi country home. Hundreds of mourners gathered on Thursday in the hometown of Nigerian novelist Chinua Achebe for the funeral of the man regarded as the father of modern African literature and the author of the widely praised 'Things Fall Apart.' AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI (Photo credit should read PIUS UTOMI EKPEI/AFP/Getty Images)

Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan

To sai dai kuma taron na yau na zaman sabuwar kafa ta sake hadewar gwamnonin da suka share sama da tsawon sa'o'i shida suna tattauna sabon rikicin tattalin arzikin dake barazana ga makomarsu gaba daya.

An dai tsara shi kansa zauren taron tare da jera kujerun shugabanin biyu a gefen juna da nufin rage tasirin rikicin dake nuna alamun in da kasar ke shirin fuskanta shekaru biyu masu zuwa. Matakin kuma da daga dukkan alamu ya kama hanyar tasiri a bangaren Rotimi Ameachi dake jagorantar 'yan 19 kuma yace ba shi da ta cewa kuma ba rabuwar kai a tsakaninsu. Da na tambaye shi shin naga kuna ta raha da su Jang shin kun shirya ne, sai ya kada baki yace ai ba rabuwa a tsakanin mu.

Muhammadu Buhari from the opposition party ANPP (All Nigeria People's Party) acknowledges support after voting in Daura, Nigeria, Saturday, April. 19, 2003. President Olusegun Obasanjo seeks a second term in elections Saturday that pose the stiffest test for Nigeria's young democracy since his election four years ago ended 15 years of military rule. (AP Photo/Schalk Van Zuydam)

Madugun 'yan adawan Najeriya, Muhammadu Buhari

To sai dai kuma ko ma wane irin tasiri ake fatan taron na iya kaiwa ga iya kokarin sake hadewar kungiyar wuri guda dai daga dukkan alamu jamiyyar PDP da 'ya'yanta ke jagorantar boren na da jan aikin iya kaiwa ga bambance abun dake cikin zuciya da abun dake bakunan gwamnonin na ta. Ko da daren jiya dai kokarin kai wa ga shugaba Jonathan a bangaren gwamna Ameachin ya hadu da cikas a yayin da jami'an tsaron fadar gwamantin suka ce ba zai iya kai wa ga teburin shugaban dake walimar rabin wa'adin mulkin sa a fadar gwamntin. Haka kuma an kai ga musayar yawu da ma kalamai zafafa a tsakanin Ameachin dake dan uwansa Godswill Akpabio na jihar Akwa Ibom kuma shugaban gwamnonin PDP.

Nigerian president Olusegun Obasanjo, speaks to Peoples Democratic Party (PDP) faithful at a rally in Lagos, Nigeria, Friday April 4, 2003. Obasanjo will be running for a second term in the up coming April 19, 2003 General Elections. (AP Photo/George Osodi)

Olusegun Obasanjo, wanda ake zargin na bayan gwamna Ameachi

Shi kansa gwamna Jang dai yace yana da ja kuma har yanzu shine ke jan ragamar gwamnonin kasar ta Najeriya na halas.

To sai dai kuma ko bayan gwagwarmayar tabbatar da ikon bangarorin biyu dai gwamnonin sun kuma ce sun zauna sun dubi jerin batutuwa da dama da suka hada da matsalar rashin kudin da ta kaisu ga bara'a da gwamantin tarrayar a cikin makon jiya, matsalar kuma da a cewar Gwamna Tanko Umar Almakura na jihar Nasarawa aka kama hanyar ganin bayan ta har abada. Abun jira a gani dai na zaman makomar rikicin da ke iya kai wa ga shafar kokarin Tarrayar Najeriya na gudanar da sahihin zabe a cikin kwanciyar hankali.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman

Sauti da bidiyo akan labarin