1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

DW ta bai wa Yulia Navalnaya lambar yabo

Abdoulaye Mamane Amadou AH
June 6, 2024

Mai dakin madugun 'yan adawar Rasha marigaye Alexey Navalny, wato Yulia Navalnaya, ta lashe kyautar fadar albarkacin baki ta tashar DW a wannan shekara.

https://p.dw.com/p/4gid3
Hoto: DW

 Navalnaya da yanzu haka ke samun mafakar siyasa tun bayan mutuwar mai gidanta a gidan kaso a watan Febrairun da ya gabata, ta bayyana manufofinta na ci gaba da dorawa daga inda majinta da ke zama daya daga cikin masu tagomashi a nahiyar Turai ya tsaya wajen tabbatar da 'yanci da walwala da kuma kare dimukuradiyya.

 Yulia Navalnaya ta kasance jaruma

Deutschland I Yulia Navalnaya in Berlin Wahlen in Russland - 2024
Hoto: Ebrahim Noroozi/AP/picture

A karkashin jagorancin wata  gidauniyar da mai gidanta Navalny ya assasa da ke yaki da cin hanci da rashuwa, DW ta karrama Yulia Navalnaya, inda babban daraktan tashar DW ya bayyana cewa gidauniyar ta taka rawar gani wajen fallasa duk wani ta'adin cin hancin gwamnatin Rasha.A yayin bikin na birnin Berlin fadar gwamnatin Jamus.