1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Za a fara zaben shugaban kasa a Yuganda

January 14, 2021

'Yan kasar Uganada na kada kuri'a a wannan Alhamis a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun dokoki inda shugaba Yoweri Museveni ke neman tazarce a karo na shidda.

https://p.dw.com/p/3ntLH
Uganda IGAD Wahlbeobachtermission
Hoto: Lubega Emmanuel/DW

Zaben da zai gudana a runfunan zabe 35,000 zai fi mayar da hankali ne kan Shugaba mai ci Yoweri Museveni wanda ke dosar shekaru 40 kan madafun iko da kuma Bobi Wine matashin mawaki da ya rikide ya zama gagarabadau din dan siyasa. Mutum miliyan 18 ake sa ran za su kada kuri'a a zaben da ke daukar hankali a ciki da wajen nahiyar Afirka.

Rahotanni sun ce an baza sojoji a manyan titunan birnin Kampala tare da daukar matakan dakile tashin hankali. A Larabar nan  kuma jama'a ta bayar da labarin cewa an katse musu intanet ta yadda shiga shafukan sada zumunta ya koma abu mai matukar wahala. Kafin ranar zaben, al'ummar kasar ta shaida tashin hankali kala-kala a wurin yakin neman zabe.