1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kokarin inganta Intanet a Afirka

Zulaiha Abubakar GAT
November 26, 2019

A yayin da wasu gwamnatocin Afirka ke kokarin dakile hanyoyin sadarwa na zamani a kasashensu, wasu kungiyoyi sun dukufa wajen yalwatar da nahiyar da hanyoyin sadarwar yanar gizo.

https://p.dw.com/p/3TkQi
Symbolbild Apps Facebook und Google Anwendungen
Hoto: picture-alliance/dpa/S. Stache

 Yayin da gwamnatocin kasashen Afirka suka tashi tsaye don yaki da kafafen sadarwar zamani ta hanyar ninka haraji da kashe intanet da kuma gangamin jan hankulan al'umma da ta guji bibiyar kafafen sadarwar zamani, a bangare guda al'umma sai kara rungumar kafafen sadarwar zamani suke a matsayin dandalinsu na bayyana ra'ayi da sukar masu mulki.

Al'umma tsakanin kasashen Afirka ta Kudu zuwa Habasha sun jajirce wajen samar da fasahar sadarwa a saukake ga mazauna karkara da birane duk da yunkurin mahukunta na dakile yaduwar hanyoyin samar da bayanai da bayyana ra'ayoyi da kuma suka gwamnati, kamar yadda Juliet Nanfuka jami'ar fasahar sadarwa tsakanin kasashen gabashi da kuma kudancin Afirka ta yi karin haske:

"Wasu daga cikin hanyoyin da al'umma da kungiyoyin suke amfani da su don yin kira ga mahukunta da su guji katse, internet sune ta hanyar ire-iren gangamin da kungiya Access take shugabanta, wanda a yanzu ta mayar da hankali wajen amfani da muryoyi don rokon jihohi su daina haifar da tasaiko a harkokin fasahar sadarwa".

Tansania Kondora Mädchenschule
Hoto: DW/N. Quarmyne

To sai dai duk wadannan kiraye-kiraye da masana harkokin sadawar ke yi, gwamnatoci na nan kan bakansu na daukar tsauraran matakai a harkar, cikin kwanakin nan gwamnatin kasar Zambiya ta bijiro da bukatar yiwa masu kallon tashar Netflix karin kudin haraji ,ita ma kasar Yuganda wacce ke yawaita yin karin kudin haraji a harkokin internet ta jefa 'yan kasarta masu mu'amala da kafafen sadarwar zamani a tsaka-mai-wuya.


sakamakon binciken da cibiyar sadarwa ta Whitehead ta gudanar ya bayyana cewar kashi 75 na al'umma Yuganda na amfani da manhajar Vitual Private Networks VPN don kauce wa harajin da hukumomin kasar suka kakaba. A wannan batu ma Jami'ar fasahar sadarwar ta yi jawabi tana mai cewa:

"An samu babban sauyi da gamsuwa a sabbin hanyoyin amfani da internet cikin sauki, da kuma bayyana albarkacin baki ba tare da fargaba ba"

Rebecca Mackinnon Internet Governance Conference in Joao Pessoa
Hoto: DW/S. Leidel

Duk da tsauraran matakan da wasu gwamnatoci suka dauka don rage watayawar bayanai a kafafen sadarwar zamani ta  hanyar amfani da Internet, na kara samun karbuwa tsakanin kasashen na Afirka. Ga dai Carlos Rey-Moreno shugaban manhajar Zenzeleni, ya bayyana muhimmancin masu wadata al'umma a kudancin Afirka da internet:

" Jama'a da dama na son bunkasa yankuna da dama ta hanyar internet, mun fara fuskantar yawan masu kai internet yankuna".


Duk da kyamar harkokin sadarwar zamani da hukumomi ke yi a kasashen Afirka, al'ummar yankunan sun dukufa wajen nemar wa kansu mafita.