Yaya Toure ya sake zama gwarzo a Afirka | Labarai | DW | 09.01.2015
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Yaya Toure ya sake zama gwarzo a Afirka

Toure, dan asalin kasar Ivory Coast wanda ke wasa wa Manchester city, ya kasance mutum na farko da ya samu wannan matsayi har sau hudu a jere a Afirka

An gabatar da shahararren dan wasan kwalon kafan nan na kasar Ivory Coast Yaya Toure a matsayin gwarzon dan wasan Afrika na wannan shekara.

Ya ce "a gaskiya, ba wai a harkar wasan kwallon kafa kawai ba, na sha fatan cinma nasara a abubuwa da dama. Sai dai a fannin wasa wannan ba abu ne mai sauki ba, musamman ma yanzu da muke da kwararrun matasa da suka shiga wannan harkar, kuma suna taka rawa mai kyau".

Tuni dai kungiyar kwallon kafa da ya ke wa wasa ta Manchesta city ta aike masa da sakon taya murna, tare da nuna alfahari da shi. Masu horar da 'yan wasa na Afrika da direktocin harkokin wasanni ne dai, suke zartar da wanda ya cancanci wannan lambar yabo na gwarzon kwallon kafar Afrika.